Albarkacin ralin mauludin Annabin Rahama (S.A.W) da za'a gudanar a karamar hukumar Kontagora a jibi lahadi, Maigirma Sanata Dakta Aliyu Sabi Abdullahi (Baraden Borgu) yabada gudunmuwar Naira Dubu Dari Hudu (N400000) ga Ahlul Darikatul Tijjaniyya na karamar hukumar Kontagora.
Sanatan ya mika wannan gudunmuwa ne ta hannun wakilin sa Alhaji Abubakar Dan Usman wanda shugaban Shababul Faila Malam Auwal Inuwa ya karba a madadin 'yan darikar.
Wannan dai bashine karon farko da Sanatan ke bada irin wannan gudunmuwa ba domin duk shekara yana bada gudunmuwarsa domin gudanar da Mauludi, Hakazalika yana tallafawa sauran kungiyoyin addini a duk lokacin da wani hidimar addini ya tashi.
Allah Ya Saka Masa Da Alkhairi. Amiin
0 comments