Daga Babangida A. Maina
Ɗaya daga cikin iyayen kungiyar Fityanul Islam ta ƙasa Sheikh Khalifa Ali Abul fath ya kai ziyara gidan yari (Prison) dake Maiduguri jihar Borno don bikin murnar zagayowar ranar haihuwan Manzon Allah (saw) da kuma bilin wasu daga cikin fursunonin.
Kamar yadda ya saɓa duk shekara a daidai wannan lokaci na Rabi'ul Awwal (watan mauludi) yakan kai ziyaran ne tare da basu kayayyakin more rayuwa da kuma yi masu nasiha da kyawawan halin irin na Manzon Allah, da kuma kyautatawa hali a tsakanin su.
Allah Ya Saka Masa Da Alkhairi. Amiin
0 comments