Saturday, November 9, 2019

WANI SENATA YA BADA GUDUMMAWAR DIBINAI DA RUWA

MAULUDIN BANA: Sanatan Neja Ta Arewa Ya Bada Gudummawar Naira Dubu 400 Da Dabino Da Ruwan Gora Ga Mabiyar Darikar Tajjaniyya

Albarkacin ralin mauludin Annabin Rahama (S.A.W) da za'a gudanar a karamar hukumar Kontagora a gobe Lahadi, Maigirma Sanata Dakta Aliyu Sabi Abdullahi (Baraden Borgu) mai wakiltar Jihar Neja ta Arewa kuma mataimakin mai tsawatarwa na majalisar dattijai, yabada gudunmuwar Naira Dubu Dari Hudu (N400000) ga mabiya Darikatul Tijjaniyya na karamar hukumar Kontagora.

Sanatan ya mika wannan gudunmuwa ne ta hannun wakilin sa Alhaji Abubakar Dan Usman wanda shugaban Shababul Faila Malam Auwal Inuwa ya karba a madadin 'yan darikar.

Sannan ya sayi katan-katan na dabino da ruwan gora domin rabawa bayin Allah da suka halarci ralin.

Wannan dai ba shi ne karon farko da Sanatan ke bada irin wannan gudunmuwa ba domin duk shekara yana bada gudunmuwar sa domin gudanar da Mauludi. Hakazalika yana tallafawa sauran kungiyoyin addini a duk lokacin da wani hidimar addini ya tashi.

Sen.Barade Media Team.
09/11/2019.

Load disqus comments

0 comments