Wata rana wani bayahude da ake kira da suna Uhban yana cikin kiwon tumaki a gefen garin madina, sai kura tazo ta cafki daya daga cikin tumakinsa sai ya bi ta da gudu, kuran ta saki tunkiyan taje ta hau kan wani dutse ta zauna akan kafafunta tace, ya Uhban shin zaka hana ni arzikin da Allah ya koro min ne, sai Uhban ya waiga yana neman mai magana amma bai ga kowa ba, sai kura ta kara nanata maganarta, da ya tabbatar da kura ce take magana, sai ya kama mamaki yana cewa, yau ga abun mamaki kura na magana, sai kura tace abinda yafi wannan mamaki shine akwai wani mutum a bayan wannan dabinon, yana ba mutane labarin abinda ya shude da abinda zai zo, duk wanda yayi imani da shi zai shiga aljanna amma kai kana nan kana kiwon tumaki, nan take Uhban ya bar tumakin da kuran ya tafi garin madina yana shiga ya tambayi mutane, shin akwai wani mutumin da yake kiran mutane zuwa wani addini banda na yahudanci a garin nan ? Sai aka ce masa eh, Muhammadu ne wanda yayi hijira daga Makka ya dawo nan Madina, yana can yana gina masallacinsa, sai yaje ya samu Annabi saw da sahabbai suna tsakiyan ginin masallaci, da ya matso kusa da Annabi sai manzon Allah yace masa, me kura ta fada maka ya kai Uhban ? Nan take Uhban ya musulunta ya furta kalmar shahada, ance ya kama wurin tumakinsa ya samu kura na masa gadi babu daya da yayi ciwon kai, ance ya yankawa kuran tunkiya daya saboda sanadin alhairi da tayi masa.
Irin wadannan tarihohin tun muna kananan yara, ba mu ma iya karatu ba muka haddace su saboda yawan jinsu da Mike yi a wuraren maulidi, har yanzu mun tasa muna iya karantawa da kanmu, wannan shine fa'idar yin maulidi.
Allah ya kashe my cikin soyayyar manzon Allah SAW amin.
Dan Allah idan ka gama karantawa kayi Comment da salatin Annabi SAW...
Rubutawa : Rayyahi Sani Khalifa
Fityanul Islam Of Nigeria
0 comments