.
• Isra’I da Mi’iraji (tafiyar da akayi dashi zuwa masallacin kudus da hawa da akayi dashi zuwa sama), Ya faru ne kafin ayi hijira zuwa Madinah da shekara uku (3), a lokacin ne aka farlanta salloli.
.
• Shekarar farko (1) bayan hijira: hijira zuwa Madinah, gina masallacinsa, fara kokarin kafa daular musulunci, farlanta Zakka.
.
• Shekara ta biyu (2): Yakin Badar babba, (a cikinsa ne Allah ya daukaka muminai ya kuma korasu akan abokan gabansu).
.
• Shekara ta uku (3): Yakin Uhud ; a wannan yakin ne musulmai suka samu rauni saboda sabawar da wasu daga cikinsu sukayi wa karantarwan Annabi da shagaltuwa wajen diban ganima.
.
• Shekara ta hudu (4): yakin "Banin-Nadiir; a wannan yakin ne Annabi ya fitar da yahudawan "Banin-Nadiir" daga Madinah saboda warware alkawari da sukayi.
.
• Shekara ta biyar (5): yakin Banil- Musdalaq, yakin Ahzab, yakin Bani- kuraiza.
.
• Shekara ta shida (6): sulhun-Hudaibiyya, kuma a wannan shekarar ne aka haramta giya har abada.
.
• Shekara ta bakwai (7): yakin Khaibar, a wannan shekarar ne Annabi da musulmai suka shiga garin Makka sukayi umara, kuma a shekarar ne ya Auri "Safiyyah" ‘yar Huyayyi.
.
• Shekara ta takwas (8) : yakin Mu’uta(tsakanin musulmai da Rumawa), fathu- Makka, yakin Hunain (tsakanin musulmai da kabilun Hawaz da sakiif).
.
• Shekara ta tara (9): yakin Tabuk; wannan shine yaki na karshe da Annabi yayi a rayuwarsa, kuma a wannan shekaran ne mutane suka zo gurin Annabi suka shiga musulunci kungiya-kungiya, shiyasa ake kirar wannan shekarar “shekarar wufudi”.
.
• Shekara ta goma (10): hajin ban-kwana, a shekarar ne Annabi yayi haji tare da musulmai sama da dubu dari.
.
• Shekara ta goma sha daya (11): a farkon wannan shekarar ne Annabi ya rasu, ya rasu ne ranar litinin cikin watan Rabi’ul- Awwal duk da cewa anyi sabani wajen kididdige kwanan watan.
.
Annabi ya rasu ne yana da shekara sittin da uku (63) a rayuwarsa,
.
Yana da Arba’in (40) daga ciki kafin ya zamo Annabi, Ashirin da uku (23) kuwa yana Annabi kuma manzo,
.
shekara goma sha uku (13) daga ciki yayi su ne a Makka, sauran goman (10) kuma a Madinah (tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi da alayensa da sahabbansa). Gaba daya
.
Ya ‘yan’uwa musulmai!!
.
Ku duba irin wannan rayuwa ta Annabi !
.
Shin haka rayuwarmu take?!!
.
Ko dai bamu sakankance bane cewa wannan Annabi shine Annabin da aka aiko mana ?!!
.
ku tuna da fadin Allah madaukakin sarki da yake cewa :
.
" Hakika kuna da abin koyi mai kyau game da ANNABI (S.A.W). [suratul Ahzab, Aya :(21)]([1])
.
Happy Maulid Nabiyi S.A.W to All lovers of S.A.W
.
Allah ya bamu Albarkacin ANNABI S.A.W bijahi S.A.W. Ameen
0 comments