Friday, November 8, 2019

BIKIN MURNAR MAULUDI


An Biyama Wata Majinyaciya Kudin Aiki (Operation) Saboda Murnar Maulidi

Daga Rayyahi Sani Khalifa

A cigaba da murnar zagayowan maulidi, Khalifa Ali AbulFathi RTA ya ziyarci babban Asibitin garin Borno, domin dubiya ga masu jinya, ziyarar ta kasance karkashin Kungiyar hadin kan zawiyoyin tijjaniyya na Maiduguri (Zawiyya Development Association), Khalif ya rarrabawa marasa lafiya tallafi. Kuma wannan Kungiya mai albarka ta dauki nauyin biyan Naira dubu 200 ga wata majinyaciyar da take da bukata.

Khalifa Ali AbulFathi ya yabawa Likitoci akan kokarin da suke yi na ceto rayukan al'umma, ya kuma yi kira ga mutane da su yawaita zuwa dubiya da bada agaji da tallafi ga marasa lafiya dake kwance a asibitoci.

Ziyarar ta samu rakiyar muqaddamai da khalifofi da almajirai na Darikar TIJJANIYYA kamar su :

*khalifa Bashir Dankellori
*Malam Muhammad Sheikh Abagoni
*Dr. Abba Sale Shekh Ahmad Abulfathi
*Dr. Jugudo
*Shugaban zakirai Zakru Lawan
*Alh Babale Gwange
*Shehu Sharif  da sauransu
*Har ilayau tasamu rakiyar kungiyoyi na Darikar *Tijjaniyya kamar su :
*Tijjaniyya Muslim students association of Nigeria (TIMSAN)
*Tijjaniyya Muslim Women development Association (TIMWODA)
*Fitiyanul Islam Of Nigeria
*Ahbabu Sheikh Ahmad Abulfathi R.A
Da sauransu
Load disqus comments

0 comments