Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, yayi kira ga Al'ummar Najeriya da su yi koyi da kyawawan halayen Manzon tsira Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wasallam.
Gwamnan Bala, yayi wannan Kiran ne a lokacin da yake jawabin sa a ranar Asabar a wajen murnar zagayowar haihuwar Annabi Muhammad Sallalahu Alaihi Wasallam, Maulidi.
Ya bayyana cewar lizimtar kyawawan halayen Annabi ko Suffofin sa zasu iya kawo karshen wadan su matsalolin sa suka dabaibaye kasar nan.
Sanata Bala, ya kuma kira ga Al'umma suyi amfani da wannan lokacin mai Albarka na Maulidi don yin Addu'oi ga kasar mu Najeriya.
Allah Ya Saka Da Alkhairi, Allah Ya Ƙara Mana Soyayyan Manzon Allah (saw). Amiin
0 comments