Friday, November 8, 2019

TSARABAR JUMMA'A
.
Tare da Umar Chobbe.
.
HIJIRAR ANNABI (S.A.W) ZUWA MADINAH :
.
Sai Annabi (S.A.W) da Abubakar (R.A) suka nufi kogon Saur suna masu hijira zuwa Madinah, suka zauna cikin kogon tsawon kwanaki uku, don haka labarinsu sai ya bace wa kuraishawa. Lokacin da Annabi da Abubakar suka shiga Madinah, sai mutanen garin suka karbe su hannu bibbiyu, sai Annabi ya gina masallacinsa da masaukinsa.
.
13. YAKUKUWAN DA ANNABI (S.A.W) YAYI A RAYUWARSA:
.
An karbo hadisi daga "Ibn Abbas" (Allah ya kara masa yarda) yace: ”lokacin da Annabi ya fita daga garin Makka yana mai hijira,
.
Sai Abubakar (R.A) yace: wadannan mutane (kuraishawa) sun shiga uku sun lalace!! Ta yaya za’ayi su fitar da Annabinsu daga garinsa!!
.
Sai Allah madaukakin sarki ya saukar da fadinsa cewa: "An yi izini ga wadanda ake yakarsu da cewa lalle an zalunce su, kuma lallai hakika Allah mai iko ne kan taimakonsu" .[suratul Hajji, Aya :(39)].
.
Itace aya ta farko data sauka tana umarni da yaki.
.
Yakukunan da Annabi (S.A.W) yayi a rayuwarsa guda Ashirin da bakwai(27) ne, wadanda yaki ya faru a cikinsu guda tara(9) ne, gasu kamar haka :
.
1.Badr.
2.Uhud.
3.Muraisi’i.
4.Khandaq.
5.Bani-kuraiza.
6. Khaibar.
7. Fathu-Makka.
8. Hunain.
9. Adda’if.
.
Kuma ya aika Sariyyah (rundunan yaki karkashin jagorancin wani sahabi) guda hamsin da shida (56).
.
Happy Maulid Nabiyi S.A.W to All lovers of S.A.W
.
Allah ya bamu Albarkacin sa bijahi S.A.W. Amiin
Load disqus comments

0 comments