"DABI'U MANZON ALLAH (SAW)" Kashi Na Ɗaya ( 1 )
.
Daga Umar Chobbe
.
Al'amarin kyawawan dabi'u al'amari ne na 'yan Adam da aka yi tarayya a kansa tsakanin mutane gaba dayansu da dukkan sabanin addinansu da nisan yankunanasu da kuma yarukansu. Mutum yana rayuwa a jama'a ne da a cikinsu akwai na nesa, da na kusa, da karami, da babba, da mace, da namiji, da mai neman sani, da malami, kuma da mai kasuwanci, da maras aiki. Mutum yana bukatar abubuwan da ta hanyar su ne zai kiyaye mu'amala da sauran mutane don cimma gurin rayuwarsa da bukatunsa kamar yadda Allah Ya yarda.
.
Don haka ne ma kyawawan dabi'u suka zama tsani domin nuna yadda ya kamata a yi mu'amala da wasu, da kuma yadda za a yi mu'amalar mutum tare da wani mutumin a bisa ka'idar "Yin mu'amala da mutane kamar yadda kake so a yi mu'amala da kai". Ko kuma "Kamar yadda ka yi za a yi maka" .
Saboda haka mutum ba ya wadatuwa gabarin wannan dabi'a da zata kare ayyukansa, ta kuma tsarkake tunaninsa, da kuma bayar da gudummuwar nisantar da kai daga ayyuka marasa kyau, domin ba komai ne ya sa aka halicci mutum ba sai domin ya samu daukaka zuwa ga kamala, da kuma gina al'ummar da adalci da taimakekeniya zasu zama su ne suke jagorantar ta domin kariya daga zalunci da fasadi.
.
Wannan shi ne abin da ake kira "Kyawawan dabi'u wato Akhlak" Wanda ya kasu zuwa na nazari da na aiki. Ta wani bangaren kuma wajibi ne a nisatar da kai daga karya, da ha'inci, da hassada, da riya, da rudin kai, da jiji da kai, da mugun kuduri, da giba, haka nan wajibi ne a siffantu da gaskiya, da amana, da burin alheri ga juna, da sauransu na daga kyawawan dabi'u da ya zama wajibi ne a kan mutum ya san su, kuma ya san munananta da kyawawanta, wannan duk ana cewa da shi Ilimin Kyawawan dabi'u na nazari.
.
Sannan sai a siffantu da su a rayuwa a aikace tare da iyalai, da 'yan'uwa, da makwabta, da wadanda suke gefe, wannan shi ne ake kira Ilimin Kyawawan dabi'u na aiki.
.
Da mun kula mun yi la'akari da zamu samu cewa mafi yawancin mutane da suka siffantu da Kyawawan dabi'u su ne annabawa, musamman Annabinmu mafi girma Muhammad (s.a.w) ta yadda ya zama yana daga sababin aiko shi, shi ne domin ya cika manyan dabi'u kamar yadda shi da kansa (s.a.w) ya shelanta, ya kasance yana siffantuwa kafin a aiko shi da mai gaskiya amintacce; saboda gaskiyar zancensa da aiki da amana har Allah madaukaki ya yabe shi da cewa: "Lallai kai kana da kyawawan dabi'u masu girma" .
.
Ashe kenan kyawawan dabi'u suna da muhimmanci mafi girma, kuma suna daga siffofin Annabawa, kuma an yi tarayya a tsakanin mutane a cikinsu, sai dai cewa mafificiyarsu kuma mafi girmansu sun tabbata ne kuma an san su ne saboda aiko fiyayyen 'yan Adam Annabi Muhammad (S.A.W).
.
Wannan makala da ta kunshi sanin kyawawan halayen musulunci, an rubuta ta ne domin dan Adam musamman musulmi ya samu tsinkayo game da dabi'un da musulunci ya zo da su, wacce yake wajibi ne ya san ta ya kuma siffantu da ita ya kuma yi aiki da ita, musamman a wannan zamani da mafi yawancin mutane suka koma tamkar dabbobi, zalunci da keta suka mamaye ko'ina, aka rasa aminci da amana, aka kuma bata sunan musulunci, ta hanyar mutane da suka karkace suka fari sabon kire ga musulunci, suka yi barna da sunan musulunci, wanda musulunci ya barranta daga garesu.
.
Musulunci addinin kyawawan dabi'u ne da soyayya da aminci da mutumtaka, kuma addini ne da yake maganin cututtukan rai, yake kuma fuskantar da mutum zuwa aljanna.
.
Muna rokon Allah madaukaki mai rahama ya sa mu dace da bin dabi'un musulunci, ya kuma ba mu ikon bayyanar da su ga mutane a wannan gajeriyar makala, ta zama kofa ga kowane mutum; domin shiga da sanin kyawawan dabi'un musulunci. Kuma muna rokon Allah ya karbi wannan aiki da kuma neman addu'a daga muminai, ya kuma sanya ladan rubuta wannan makala ga kakannina kamar Shaikh Sa'id da malam Husain da shaikh Usman.
.
Happy Maulid of Nabiyi S.A.W
.
Allah ya bamu Albarkan ANNABI S.A.W. Ameen