Monday, December 9, 2019

Maulana Sheikh Dahiru Usman Bauchi

LISANUL-FAIDHATI(Maulana Sheikh Dahiru Usman Bauchi) Yana Cewa:
:
"Ku Sani Fa; Dukkan Wanda Aka Ce Masa Ya Shiga 'DARIQA Yaqi To Ba Fa Shi Ne Yaqi Ba, A'a ALLAH Ne Bai So Shi Da Hakan Ba, Dalili Kuwa Shi Ne; Dukkan Wani Abu Mai Tsada ALLAH(S.W.T) Ya Kan Ke6e Wasu Za6a66u Ne Daga Cikin BayinSa Ya Ba Su Aikin,
:
To Ita Dai 'DARIQA Aikinta Na Farko Shi Ne;
:
*. YAWAN TUBA; Inda ALLAH Da KanSa Yake Shelantawa BayinSa Cewa Duk Mai Yawan Tuba, To ALLAH Yana Sonsa In Ji ALLAH(S.W.T) Yana Cewa:"Innallaha Yuhibbu Tawwabin".
:
Aiki Na Biyu; A 'DARIQA Shi Ne SALATIN ANNABI(S.A.W) Lazim Ne, Kuma Ba Mai Yawan Yi Ma ANNABI(S.A.W) Salati Sai 'MUMINI' Domin Da ALLAH(S.W.T) Ya Zo Yin Gayyar Ayi Salatin Bai 'Kira Kowanne Tarkace Ba, A'a Cewa Yayi Ya Ku Masu 'IMANI' Ku Yi Ma ANNABI Salati;"Innalla
ha Wa Mala'ikatahu Yusalluna Alan Nabiy Ya Ayuhallazina 'AMANU' Sallu Alaihi Wasallimu Taslima",
:
Aiki Na Uku Shi Ne;'Lailaha IllalLah.......
............', Saboda Tsadar Wannan Kalma Da Zaka Shekara 'Dari Kana Kafiri Amma Ka Fad'e Ta Rana 'Daya Tak, Ka Cika(Mutu) Da Ita, Da Shike Nan Kafircin Nan Na Shekara 'Dari Ya Rushe Ka Zama 'Dan Aljannah,
:
To Wannan Kalma Ita Ce Ko Yaushe 'Yan Tijjaniya Suke Cikawa Da Ita, Domin Lokacin Rayuwarsu a Kullum Cikin Fadinta Suke Yi Safiya Da Maraice.
:
Duk Wanda Ya Samu Kansa a Da'irar/Cikin 'Dariqar Tijjaniyya Sai Yayi Godiya Ga UBANGIJI Da Ya Zabe Shi a Cikin BayinSa Za6a66u, Ya Kiyaye Ta".
:
ALHAMDULILLAH ALLAH MUN GODE!
:
MU DAI FATANMU A KULLUM SHI NE ALLAH YA QARAWA MAULANMU LAFIYAR(Jiki) DA JURIYA, YA KUMA QARA MANA SONSU DA'IMAN AMEEEEN
Continue reading...

Monday, December 2, 2019

Kyawawan Dabi'un Manzon Allah (saw)

DABI'UN ANNABI S.A.W (Part 2)
.
Daga Umar Chobbe
.
Kyawawan Dabi'u

Kyawawan dabi'u su ne ruhin shari'a, kuma asasin addini, babu wani Annabi da ya zo sai da ya yi kira tsakanin mutane da kyawawan dabi'u, da kuma tilascin tsarkake su daga abin da yake iya kai su ga aikata munanan dabi'u, da kuma nesantar da su daga abin da yakan iya lalata hadafinta, sai ya zana mana tafarki da hanya, ya gina mana dokoki da zamu yi amfani da su domin kawo canji ga mutum zuwa ga mafi kamalar samuwa wacce mutum zai dogara da ita domin ya kai ga matsayi mai girma na kyawawan halayen, ya kuma zamanto daga zababbu tsarkaka daga bayinsa.
.
Ilmin Kyawawan Dabi'u

Ilmin kyawawan dabi'u ilmi ne da yake da ma'auni da za a iya dogara da shi, shi ne tattararrun dokoki da ya kamata dabi'ar dan Adam ta kasance a kanta bisa wadannan dokokin kamar yadda aka gindaya a zance ko a aiki ko a zuciya. Da wadannan ma'aunai zamu zana hanyar kyawawan dabi'u abin yabo, mu kuma yi kokarin iyakance hadafinsu da abubuwan da suka ginu a kan su.
.
Kyawawan Dabi'un Musulunci
Dabi'un musulunci su ne tattararrun zantuttuka da ayyuka na zahiri da na badini da suka doru bisa ka'idoji, da kuma ayyuka madaukaka da ladubban da suka doru a kansu, wadanda suka dogara a kan akida da shari'ar musulunci da dogaro mai karfi daga kur'ani mai girma da sunnar Manzon Allah (s.a.w) da imamai tsarkaka (a.s). Kyawawan dabi'u a musulunci ba komai ba ne sai bangare na addini, kai shi ne kashin baya da ruhin addini ma .
.
Allah ya bamu Albarkan ANNABI S.A.W. Ameen
Continue reading...

Jerin Sunayen Sarakunan Da Dan'fodio Ya Basu Tuta

Jerin Sunayen Sarakunan Da Sheik Usman Dan Fodio Ya Ba Su Tuta.

Daga Babangida A. Maina

1- Modibbo Adama→Adamawa
2- Malam Umaru Dallaji→ Katsina
3- Malam Yakubu→ Bauchi
4- Malam Suleman → Kano
5- Malam Isiyaku → Daura
6- Malam Buba Yero → Gombe
7- Malam Gwani Mukhtar → Misau
8- Malam Sambo → Hadeja
9- Malam Dendo → Nupe
10- Malam Musa → Zazzau
11- Malam Alimi → illorin
12- Malam Ibrahim Zaki → Katagunm
13- Malam Dan Tunku → Kazaure
14- Malam Muhammad Wabi → Jama'are
15- Malam Sambo Dan Ashafa → Gusau

Wadannan sune Sarakuna kuma Malamai wadanda Shehu Usman Dan Fodio ya ba su tuta kowanne da kasarsa.

ALLAH YA JIKAN SU DA RAHMA. ALLAH YA BASU GIDAN ALJANNAH. AMEEEEN
Continue reading...

Thursday, November 28, 2019

Sheikh Aliyu Harazumi Kano

Wata Rana

SHEIKUL ALIYU HARAZIMI (RA) Yana bincike a Wani Littafi Na SIDI ABDULQADIR JAILANI (RA)
:
Sai Ya gani a Cikin Wannan Littafi inda SIDI ABDULQADIR (RA) Yana Cewa;
:
Duk Wanda Ya Karbi Darikar QADIRIYYAH Take agun Ya Zama QUTHBI Tun Kafin Ya Fara WURIDANTA.
:
Sai SHEHU ALIYU HARAZIMI (RA) Ya Kawo Wannan Magana gun SHEIK AHMAD TIJJANI (RA).
:
Sai KHUTBUL MAKHTUM Ya Ce Masa Haka ne Wannan Magana amma nawa DARIQAR Duk Wanda Ya Shigeta Darajarsa ta Kai na KHUTBAI Guda DUBU.
:
ALHAMDULLILAH!!!
:
Domin Duk Wani WALIYYI Komin Girmansa Yana Sha ne Daga KOGIN KHUTBUL MAKTUUM.
:
ALLAH YA KASHE MU MUNA TIJJANIYYA NA GISKIYA BA NA DA'AWA BA. AMEEN
Continue reading...

Kana Son Zama Abokin Zaman Manzon Allah A Cikin Aljannah?

TSARABAR JUMMA'A
.
Tare Da Umar Chobbe.
.
KANA SON ZAMA ABOKIN ZAMAN ANNABI S.A.W. A CIKIN ALJANNA?.
.
Annabi S.A.W. Yace: "Duk Wanda Yayimin Salati Aboye Zai Zamo Abokin Zama Na A Aljanna.
.
Amma Wanda Yayi A Bayyane Kowa Yana Ji; Annabi S.A.W. Zai Tashi Ranar Qiyama Yacema Allah Azza Wajalla "Ya Ubangiji Wannan Yayi Min Salati A Bayyane A Duniya Inaso Ayi Masa Gafara, Sai Allah Ya Biya Haqqoqin Dake Kanka Allah Ya Biya Maka.
.
Sannan Kuma Duka Ibadunka Allah Zai Karba" Saboda Kayi Salatin Annabi Muhammadu S.A.W. A Bayyane;
.
Saboda Haka Mu Saba Da Yawaita Salatin Annabi S.A.W. Ako Da Yaushe;
.
Allahumma Salli Ala Sayyidina Muhammadin Wa Ala Alihi Haqqa Qadrihi Wa Miqdarihil Azeem.
.
Allah Ya Barmu Da ANNABI S.A.W. Amiin
Continue reading...

Wednesday, November 27, 2019

Dabi'un Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama

"DABI'U MANZON ALLAH (SAW)" Kashi Na Ɗaya ( 1 )
.
Daga Umar Chobbe
.
Al'amarin kyawawan dabi'u al'amari ne na 'yan Adam da aka yi tarayya a kansa tsakanin mutane gaba dayansu da dukkan sabanin addinansu da nisan yankunanasu da kuma yarukansu. Mutum yana rayuwa a jama'a ne da a cikinsu akwai na nesa, da na kusa, da karami, da babba, da mace, da namiji, da mai neman sani, da malami, kuma da mai kasuwanci, da maras aiki. Mutum yana bukatar abubuwan da ta hanyar su ne zai kiyaye mu'amala da sauran mutane don cimma gurin rayuwarsa da bukatunsa kamar yadda Allah Ya yarda.
.
Don haka ne ma kyawawan dabi'u suka zama tsani domin nuna yadda ya kamata a yi mu'amala da wasu, da kuma yadda za a yi mu'amalar mutum tare da wani mutumin a bisa ka'idar "Yin mu'amala da mutane kamar yadda kake so a yi mu'amala da kai". Ko kuma "Kamar yadda ka yi za a yi maka" .
Saboda haka mutum ba ya wadatuwa gabarin wannan dabi'a da zata kare ayyukansa, ta kuma tsarkake tunaninsa, da kuma bayar da gudummuwar nisantar da kai daga ayyuka marasa kyau, domin ba komai ne ya sa aka halicci mutum ba sai domin ya samu daukaka zuwa ga kamala, da kuma gina al'ummar da adalci da taimakekeniya zasu zama su ne suke jagorantar ta domin kariya daga zalunci da fasadi.
.
Wannan shi ne abin da ake kira "Kyawawan dabi'u wato Akhlak" Wanda ya kasu zuwa na nazari da na aiki. Ta wani bangaren kuma wajibi ne a nisatar da kai daga karya, da ha'inci, da hassada, da riya, da rudin kai, da jiji da kai, da mugun kuduri, da giba, haka nan wajibi ne a siffantu da gaskiya, da amana, da burin alheri ga juna, da sauransu na daga kyawawan dabi'u da ya zama wajibi ne a kan mutum ya san su, kuma ya san munananta da kyawawanta, wannan duk ana cewa da shi Ilimin Kyawawan dabi'u na nazari.
.
Sannan sai a siffantu da su a rayuwa a aikace tare da iyalai, da 'yan'uwa, da makwabta, da wadanda suke gefe, wannan shi ne ake kira Ilimin Kyawawan dabi'u na aiki.
.
Da mun kula mun yi la'akari da zamu samu cewa mafi yawancin mutane da suka siffantu da Kyawawan dabi'u su ne annabawa, musamman Annabinmu mafi girma Muhammad (s.a.w) ta yadda ya zama yana daga sababin aiko shi, shi ne domin ya cika manyan dabi'u kamar yadda shi da kansa (s.a.w) ya shelanta, ya kasance yana siffantuwa kafin a aiko shi da mai gaskiya amintacce; saboda gaskiyar zancensa da aiki da amana har Allah madaukaki ya yabe shi da cewa: "Lallai kai kana da kyawawan dabi'u masu girma" .
.
Ashe kenan kyawawan dabi'u suna da muhimmanci mafi girma, kuma suna daga siffofin Annabawa, kuma an yi tarayya a tsakanin mutane a cikinsu, sai dai cewa mafificiyarsu kuma mafi girmansu sun tabbata ne kuma an san su ne saboda aiko fiyayyen 'yan Adam Annabi Muhammad (S.A.W).
.
Wannan makala da ta kunshi sanin kyawawan halayen musulunci, an rubuta ta ne domin dan Adam musamman musulmi ya samu tsinkayo game da dabi'un da musulunci ya zo da su, wacce yake wajibi ne ya san ta ya kuma siffantu da ita ya kuma yi aiki da ita, musamman a wannan zamani da mafi yawancin mutane suka koma tamkar dabbobi, zalunci da keta suka mamaye ko'ina, aka rasa aminci da amana, aka kuma bata sunan musulunci, ta hanyar mutane da suka karkace suka fari sabon kire ga musulunci, suka yi barna da sunan musulunci, wanda musulunci ya barranta daga garesu.
.
Musulunci addinin kyawawan dabi'u ne da soyayya da aminci da mutumtaka, kuma addini ne da yake maganin cututtukan rai, yake kuma fuskantar da mutum zuwa aljanna.
.
Muna rokon Allah madaukaki mai rahama ya sa mu dace da bin dabi'un musulunci, ya kuma ba mu ikon bayyanar da su ga mutane a wannan gajeriyar makala, ta zama kofa ga kowane mutum; domin shiga da sanin kyawawan dabi'un musulunci. Kuma muna rokon Allah ya karbi wannan aiki da kuma neman addu'a daga muminai, ya kuma sanya ladan rubuta wannan makala ga kakannina kamar Shaikh Sa'id da malam Husain da shaikh Usman.
.
Happy Maulid of Nabiyi S.A.W
.
Allah ya bamu Albarkan ANNABI S.A.W. Ameen
Continue reading...

Shan Bawalin Annabi Muhammadu (saw)

SHAN BAWALIN ANNABI (S.A.W)
.
Daga Umar Chobbe
.
Watarana Ummu Aimana tace: ANNABI S.A.W ya tashi a wani dare ya dauki kasko yayi bawali a ciki, bayan ya kammala sai ya mai dashi ya Ajiye, to ni kuma sai na tashi cikin dare ina jin kishin ruwa, kawai sai na shanye Abinda ke cikin kaskon
.
Ni kuma ban san cewa Bawali bane, yayin da ANNABI (S.A.W) ya tashi da Asuba sai yace dani "Ummu Aimana" tashi kije ki zubar da abunda ke cikin kaskon nan
.
Sai tace Wallahi Ya Rasulullah na Shanye Abinda ke cikin wannan kaskon
.
Sai ANNABI S.A.W yayi Murmushi har sai da perorinsa suka fito a fili
.
Sannan sai yace Wallahi kin Rabu da Ciwon Ciki kenan Kuma Wallahi cikin ki bazai sake ciwo ba har Abada. Inji ANNABI S.A.W fa jama'a
.
Duba Littafin "MAWAHIB" Malam Kasdalani ya kawo kissan aciki
.
Ina Masu cewa wai Annabi S.A.W Mutum ne kamar kowa? To kuma sai kuyi bawali ku sha har muga ko zai muku Magani. Ni dai Umar chobbe ina baku shawara da ku daina hada kanku da ANNABI S.A.W in dai kuna son zaman lafiya
.
Umar Chobbe nake ce muku Happy Maulid Of Maulana ANNABI S.A.W to All Lovers of S.A.W
.
Allah dan ANNABI S.A.W ka kara mana Son ANNABI S.A.W tare da ganin haqiqar Girman sa Zahiri da Badini. Ameen
Continue reading...

Monday, November 25, 2019

MU'UJIZAR MANZON ALLAH

MU'UJIZA : Kura Tayi Magana Saboda Shaida Risalar Manzon Allah SAW

Wata rana wani bayahude da ake kira da suna Uhban yana cikin kiwon tumaki a gefen garin madina, sai kura tazo ta cafki daya daga cikin tumakinsa sai ya bi ta da gudu, kuran ta saki tunkiyan taje ta hau kan wani dutse ta zauna akan kafafunta tace, ya Uhban shin zaka hana ni arzikin da Allah ya koro min ne, sai Uhban ya waiga yana neman mai magana amma bai ga kowa ba, sai kura ta kara nanata maganarta, da ya tabbatar da kura ce take magana, sai ya kama mamaki yana cewa, yau ga abun mamaki kura na magana, sai kura tace abinda yafi wannan mamaki shine akwai wani mutum a bayan wannan dabinon, yana ba mutane labarin abinda ya shude da abinda zai zo, duk wanda yayi imani da shi zai shiga aljanna amma kai kana nan kana kiwon tumaki, nan take Uhban ya bar tumakin da kuran ya tafi garin madina yana shiga ya tambayi mutane, shin akwai wani mutumin da yake kiran mutane zuwa wani addini banda na yahudanci a garin nan ? Sai aka ce masa eh, Muhammadu ne wanda yayi hijira daga Makka ya dawo nan Madina, yana can yana gina masallacinsa, sai yaje ya samu Annabi saw da sahabbai suna tsakiyan ginin masallaci, da ya matso kusa da Annabi sai manzon Allah yace masa, me kura ta fada maka ya kai Uhban ? Nan take Uhban ya musulunta ya furta kalmar shahada, ance ya kama wurin tumakinsa ya samu kura na masa gadi babu daya da yayi ciwon kai, ance ya yankawa kuran tunkiya daya saboda sanadin alhairi da tayi masa.

Irin wadannan tarihohin tun muna kananan yara, ba mu ma iya karatu ba muka haddace su saboda yawan jinsu da Mike yi a wuraren maulidi, har yanzu mun tasa muna iya karantawa da kanmu, wannan shine fa'idar yin maulidi.

Allah ya kashe my cikin soyayyar manzon Allah SAW amin.

Dan Allah idan ka gama karantawa kayi Comment da salatin Annabi SAW...
 
Rubutawa : Rayyahi Sani Khalifa
Fityanul Islam Of Nigeria
Continue reading...

Sunday, November 24, 2019

Mu Leqa, Mu Gano

MU LEQA, MU GANO:
:
A Lokacin Da Turawan Mulkin Mallaka Na Kasar Italiya Za Su Kashe Mujaddadi Kuma Mujahidi Sheikh Omar Mukhtar(R) Akan 'Kin Sallama Musu Da Yayi, Akan Mamayar Da Suka Yiwa Kasarsa Libya.
:
Sun Ba Shi Umarni Da Yayi Kalamai Na 'Karshe a Rayuwarsa(Kafin Su Rataye Shi), Sun Zaci Zai Roqe Su Da Su Yi Masa Rai(Kar Su Kashe Shi), Cikin Mamaki Sai Ya Fuskance Su Suka Ji Ya Ce:
:
"Daga ALLAH Mu Ke, Kuma Gare Sa Za Mu Koma".
:
Sheikh Omar Mukhtar(R) Tsayayyen 'Dan Gwagwarmaya Ne Da Yayi Yaqi Tuquru Da Mamayar Zalunci Da Turawan Italiya Suka Yiwa Kasarsa Libya, Daga 'Karshe Turawan Na Italiya Sun Rataye Sheikh Omar Mukhtar a Bainar Jama'a(Magoya Bayansa) Wanda Yayi Sanadiyar Shahadarsa a Shekarar 1931.
:
YA SALAAM!
:
ALLAH YA BA MU ALBARKAR MASU ALBARKA AMEEEEEN.
Continue reading...

Saturday, November 23, 2019

Shin Annabi Muhammadu Yayi Darika ???

SHIN ANNABI(S.A.W) YAYI 'DARIQA???
;
Tambayar Da Wani Bawan ALLAH Ya Yiwa MAULANMU SHEHU DAHIRU USMAN BAUCHI, Ga Amsar Da SHEHU Ya Bashi Kamar Haka:

* Source By Sayyadi Othman Muhammad.

"Wai Wai Wai Babbar Magana Ka San Kuwa Abinda Ake Nufi Da 'Dariqa, Ma'anar 'Dariqa Fa Shi Ne; Kamun 'Kafa Da Wani Bawan ALLAH Yayi Maka Jagora Zuwa Fadar MANZON ALLAH(S.A.W), To ANNABI(S.A.W) 'Kafan Waye Zai Kama??? Ai Shi Ne Abin Neman,
:
ALLAH(S.W.T) Da Kansa Yana Cewa; Duk Mai Nema NA(S.W.T) To Ya Nemi ANNABI MUHAMMAD(S.A.W) Ya Same NI(S.W.T);
;
"Qul In Kuntum Tuhibbunallaha Fattabi'uni Yuhibbukumullah".
;
SHEHU Ya Ci Gaba Da Cewa;"Ai Shiga 'Dariqa Laluri Ne, Domin Ko Ni 'DAHIRU USMAN BAUCHI(Afwan Maulaya) Da Na Yi Zamani Da MA'AIKI(S.A.W) 'Dariqar Wa Zan Yi, Ai Da Sahabi Zan Zama Ga SHUGABANMU(S.A.W) Ga Ni Kusa Da SHI(S.A.W), Ai Ba'a Shiga 'Dariqa(a Zamanin ANNABI(S.A.W), Amma Mun Zo Duniya Zamani Yayi Nisa Yau Ku San Shekara Dubu Da 'Dari Biyar Da Wafatin MANZON ALLAH(S.A.W) Ai Dole Mu Bi Magadan ANNABI(S.A.W) Sune; Bayin ALLAH Waliyyai Masana Hanya Su Mana Jagora Zuwa Fadar MANZON ALLAH(S.A.W), MANZON ALLAH(S.A.W) Kuma Ya Kaimu Fadar ALLAH(S.W.T), Shi Yasa Idan Ka Bisu Da Farko Sai Su Baka; ISTIGHFARI Idan Ka Yi ISTIGHFARI Sai Ka Rabu Da Shaid'an Ka Rabu Da Zunubi, Su Baka Salatin ANNABI(S.A.W) Sai Ka Samu Shiga Fadar MANZON ALLAH(S.A.W) Daga Yawan Yi Masa Salati, Sai Su 'Kara Maka Da; LA'ILAHA ILLALLAH........ Shi Ne Tikitin Shiga Aljanna Kuma Maganin Mutuwa Da Imani Wadannan Sune Aikin Da 'YAN 'DARIQU Suke Bayarwa In Ka Ji An Ce; 'DARIQA Ma'ana Hanya Zuwa Ga Zikirin ALLAH Ainihin Manufar Kenan 'DARIQA Matakala Ce Zuwa Ga Abin Nema Shi Ne Zikirin ALLAH".
;
YA ALLAH! KA QARA TABBATAR DA MU DA ZURI'ARMU BAKI 'DAYA AKAN WANNAN TAFARKIN(Na Tijjaniya),
;
SHEHU Alkhairi Ne!
;
Mun Gode SHEHU!
:
FATANMU A KULLUM SHI NE ALLAH YA QARAWA MAULANMU SHEIKH LAFIYAR(Jiki) DA JURIYA, YA ALLAH KA QARA KARE MANA SHI DA KARIYAR NAN TAKA AMEEEEN.
Continue reading...

Thursday, November 21, 2019

Sheikh Dahiru Usman Bauchi Yayi Kira Ga Barrack Obama Da Queen Elizabeth Dasu Dawo Addinin Su Nada (Addinin Musulunci)

SHEIKH TAHIR USMAN BAUCHI YAYI KIRA GA BARRACK OBAMA DA SARAUNIYAR INGILA DA SU DUBA GIRMAN ALLAH SU DAWO ADDININSU NA MUSULUNCI..

Daga Yusuf Adamu Abdullahi.

Shahararren Malamin Addinin Musulunci Kuma Babban Jagora A Cikin Darikar Tijjaniya Shekh Dahiru Usman Bauchi Yayi Qira Da Babban Murya Ga Barrack Obama Da Kuma Sarauniyar Kasar Ingila Queen Elizebeth Da Su Dawo Addininsu Na Musulunci..

Sheikh Yayi Wannan Jawabine Adaidai Lokacinda Yake Zantawa Da 'Yan Jarida A Gidansa Dake Cikin Birnin Bauchi, Inda Yake Miqa Saqon Bangajiya Wa Masu Halartarn Mauludi,

Sheikh Yace "Ina Kira Ga Barrack Obama Tsohon Shugaban Kasar Amurka Da Ya Duba Girman Allah Ya Dawo Addinin Kakanninsa Ya Kuma Duba Irin Baiwa Da Allah Ya Masa Ace Kasa Kamar Na Amurka Yana Dan Afrika Allah Ya Bashi Mulkinta Ba Don Wayonsa Ko Wata Dabara Tashiba, Kuma Ya Gama Lami Lafiya Cikin Amincewar Allah, Sheikh Yace "Ga Wani Ko Shekara Hudu Baiyiba Ana Kokarin Tsigeshi,  Sheikh Yace "Dukkanin Yan Uwanka Musulmine Kuma Wannan Abu Da Allah Ya Maka Ya Kamata Ka Dawo Ka Bauta Masa, Zamuyi Matuqar Farin Ciki Idan Muka Ganka A Addini Na Jinqai Da Zaman Lafiya..

A Karshe Sheikh Ya Qara Yin Kira Da Babban Murya Yace "Kuyiwa Allah Ku Isarmin Ga Sarauniyar Ingila "Queen Elizebeth" Da Ta Duba Girman  Allah Da Dawo Addinin Kakanninta, Sheikh Yace "Allah Ya Miki Tarin Baiwa Kin Mulki Kasar Ingila Tun Kinada Kanana Shekaru Sama Da Shekara 60 Kina Wannan Mulki Kin More Matuqar Morewa A Wannan Duniya Babu Babban Arziki Da Zaki Kara Morewa A Lahira Fiye Da Morewarki Na Duniya Kamar Wannan Addini Na Musulunci'  Sheikh "Yace Zamu Fiki Farin Ciki Idan Kika Shigo Wannan Addini Munada Tarihinki Yan Uwanki Labarabawane Kuma Musulmi Yakamata Ki Duba Wannan Kira Tawa Ki Shigo Musulunci..

Sheikh Yace Muna Roqa Musu Allah Ya Musu Arziki Da Wannan Addini Da Manzon Allah (S.A.W) Yazo Mana Dashi..


Continue reading...

Saturday, November 16, 2019

Muhimman abubuwa da suka faru lokacin rayuwar Annabi Muhammadu (saw)

MUHIMMAN ABUBUWAN DA SUKA FARU A RAYUWAR ANNABI (S.A.W):
.
• Isra’I da Mi’iraji (tafiyar da akayi dashi zuwa masallacin kudus da hawa da akayi dashi zuwa sama), Ya faru ne kafin ayi hijira zuwa Madinah da shekara uku (3), a lokacin ne aka farlanta salloli.
.
• Shekarar farko (1) bayan hijira: hijira zuwa Madinah, gina masallacinsa, fara kokarin kafa daular musulunci, farlanta Zakka.
.
• Shekara ta biyu (2): Yakin Badar babba, (a cikinsa ne Allah ya daukaka muminai ya kuma korasu akan abokan gabansu).
.
• Shekara ta uku (3): Yakin Uhud ; a wannan yakin ne musulmai suka samu rauni saboda sabawar da wasu daga cikinsu sukayi wa karantarwan Annabi da shagaltuwa wajen diban ganima.
.
• Shekara ta hudu (4): yakin "Banin-Nadiir; a wannan yakin ne Annabi ya fitar da yahudawan "Banin-Nadiir" daga Madinah saboda warware alkawari da sukayi.
.
• Shekara ta biyar (5): yakin Banil- Musdalaq, yakin Ahzab, yakin Bani- kuraiza.
.
• Shekara ta shida (6): sulhun-Hudaibiyya, kuma a wannan shekarar ne aka haramta giya har abada.
.
• Shekara ta bakwai (7): yakin Khaibar, a wannan shekarar ne Annabi da musulmai suka shiga garin Makka sukayi umara, kuma a shekarar ne ya Auri "Safiyyah" ‘yar Huyayyi.
.
• Shekara ta takwas (8) : yakin Mu’uta(tsakanin musulmai da Rumawa), fathu- Makka, yakin Hunain (tsakanin musulmai da kabilun Hawaz da sakiif).
.
• Shekara ta tara (9): yakin Tabuk; wannan shine yaki na karshe da Annabi yayi a rayuwarsa, kuma a wannan shekaran ne mutane suka zo gurin Annabi suka shiga musulunci kungiya-kungiya, shiyasa ake kirar wannan shekarar “shekarar wufudi”.
.
• Shekara ta goma (10): hajin ban-kwana, a shekarar ne Annabi yayi haji tare da musulmai sama da dubu dari.
.
• Shekara ta goma sha daya (11): a farkon wannan shekarar ne Annabi ya rasu, ya rasu ne ranar litinin cikin watan Rabi’ul- Awwal duk da cewa anyi sabani wajen kididdige kwanan watan.
.
Annabi ya rasu ne yana da shekara sittin da uku (63) a rayuwarsa,
.
Yana da Arba’in (40) daga ciki kafin ya zamo Annabi, Ashirin da uku (23) kuwa yana Annabi kuma manzo,
.
shekara goma sha uku (13) daga ciki yayi su ne a Makka, sauran goman (10) kuma a Madinah (tsira da amincin Allah su tabbata a gareshi da alayensa da sahabbansa). Gaba daya
.
Ya ‘yan’uwa musulmai!!
.
Ku duba irin wannan rayuwa ta Annabi !
.
Shin haka rayuwarmu take?!!
.
Ko dai bamu sakankance bane cewa wannan Annabi shine Annabin da aka aiko mana ?!!
.
ku tuna da fadin Allah madaukakin sarki da yake cewa :
.
" Hakika kuna da abin koyi mai kyau game da ANNABI (S.A.W). [suratul Ahzab, Aya :(21)]([1])
.
Happy Maulid Nabiyi S.A.W to All lovers of S.A.W
.
Allah ya bamu Albarkacin ANNABI S.A.W bijahi S.A.W. Ameen
Continue reading...

Friday, November 15, 2019

TSARABAR JUMMA'A

TSARABAR JUMMA'A
.
HAKURI
.
Duk masoyin ANNABI S.A.W yakamata Ya koyi hakuri don ANNABI S.A.W mahakurcine kadan daga hakurici
.
Watarana yana bacci sai wani kafiri yazo ya tada ci yana borin shewa nadade ina nemanka don in kashe ka kuma yau kariyan ka ta kare Ina mai shetanka yau
.
Wannan Mutumin dai yayi tayin borin sa yagama sai yazaro tokobinsa danufin zai Apkawa ANNABI S.A.W sai nantake wannan tokobin hannun kafirin ya dawo hannun S.A.W
.
Sai yace masa Ni ubangijina yaceceni kaifa waye zai ceceka?
.
Sai makarerren Mutumin yace babu mai cetana
.
YA RASULALLAHI yace mai toh ka karbi musulunci yace baran karbi musulunci ba
.
Sai ANNABI S.A.W yace masa toh me kake so?
.
Sai Mutumin yace ka yafeni ka barni in tafi
.
Sai ANNABI S.A.W yace masa na yafeka tashi katafi
.
Haka ya bashi tokobin sa ya tashi ya tafi kun ga Hakuri irin na ANNABI S.A.W
.
Dan uwana muma muyi Kokari mu Koyi hakuri don musamu yardan ANNABI S.A.W
.
Umar Chobbe nake ce muku Happy Maulid Of Maulana ANNABI S.A.W to All Lovers of S.A.W
.
Allah ka bamu ikon yin Hakuri acikin dukkan Lamuran Mu na yau da Kullum Albarkan ANNABI S.A.W. Ameen
Continue reading...

BABBAR MAGANA

PROFESSOR Ibrahim Ahmad Maqary Zaria (Rta) Yana cewa;
.
Daga Umar Chobbe
.
Wallahi'Yan uwa ku kiyayi kanku da
aibata wasu mutane a wuraren Maulidi da cewa;
.
"wai basa son ANNABI (Sallallahu Alaihi Wasallam), wannan kuskure ne babba, domin kalmar shahada ta hadamu da duk wanda ya amsa suna "Musulmi"
.
Don haka su din ma kuskure ne da rashin fahimta yasa ba suyin maulidin, tayiwu duk ranar da suka gane cewa ashe fa maulidin nan alkhairi ne babba, to kai da kake gadara ko tutiya kanayi idan ba kayi da gaske ba sai sunzo sun fika hidima da samun muradi acikin maulidin.
.
Mu bama fada da kowa, kuma bama gaba da kowa, kuma bama qin kowa sai dai idan mutum yazo mana da wani abu ko halayya wanda ya saba da Shari'a da kuma Manhajin da muke kai
.
Hakan ma fa ba wai mutumin zamu qi ba, A'a halin nasa ko abin da yakeyi zamu Qi
.
Domin shi din bawan Allah ne kuma dole muyiwa bawa duban Maigidansa", Alhamdulillah.
.
Allah ya karawa PROFESSOR Lafiya da Nisan Kwana Albarkan ANNABI S.A.W. Ameen
Continue reading...

Sunday, November 10, 2019

KU DUBA WANNAN GIRMA

KU DUBA WANNAN GIRMA:-
:
Wata Rana Sayyidah Fatimah(A.S) Ta Je Wajen ABBANTA{S.A.W} Da Ya Kalleta Sai Ya Ga Alamar Yunwa a Tare Da Ita, Har Fuskarta Tayi Fari.
:
Nan Take Sai Ya 'Dauki Hannunsa Mai Albarka Ya Shafa Akan Fuskarta Yayi Mata Addu'ah!
:
Sai Wacce Ta Ruwaito Hadisin Nan Ta Ce:"NAN TAKE SAI NAGA FUSKARTA TA CICCIKO TA KOMA YADDA TAKE, JIKINTA YA QARA HASKE..... SAI BAYAN WASU SHEKARU DA MUKA HADU DA ITA SAI NA TAMBAYETA:
:
"Ya Shugabata! Yaya Addu'ar Nan Wacce Abbanki Yayi Miki?''
:
Sai Ta Ce:"WALLAHI TUN DAGA WANNAN RANAR HAR ABADA
BAN SAKE JIN QISHIRWA KO YUNWA BA".
:
SALLALLAHU ALAIKA WA SALLAAM!
:
ALLAH MUNA TAWASSULI DA ALBARKACIN TAFIN HANNAYEN ANNABI(S.A.W) MASU ALBARKA KA BA MU LAFIYA DA ZAMAN LAFIYA, KA YI MANA MAGANIN ABINDA YA FI QARFINMU AMEEEN.
Continue reading...

AL'UMMAR MUSULMI SUN KARU A MASALLACI DON MURNA DA ZAGAYOWAR RANAR HAIHUWAN MANZON ALLAH (SAW) A ƘASAR TURKIYYA

Turkawa sun cika Masallatai domin tunawa da ranar haihuwar fiyeyyen halitta.


Miliyoyin Turkawa sun yi cincirindo zuwa Masallatan juma’a dake fadin kasar domin tunawa da zagayowar ranar haihuwa annabi Muhammad (SAW) watau Mawlid an-Nabi

Turkawa sun cika Masallatai domin tunawa da ranar haihuwar fiyeyyen halitta
Miliyoyin Turkawa sun yi cincirindo zuwa Masallatan juma’a dake fadin kasar domin tunawa da zagayowar ranar haihuwa annabi Muhammad (SAW) watau Mawlid an-Nabi.
An haihi Annabi Muhammad ne a Makkah dake kasar Saudiyya a shekarar 570 A.D. Musulmi a fadin duniya suna gudanar da bukuwan ranar haihuwar manzo a ko wace ranar 12 ga watan Rabi' al-Awwal, wata na uku a cikin watannin Musulunci.

Ranar dai yana sauyawa daga kasa zuwa wata kasa kasancewar yadda kasashe da dama yanzu na amfani da kalandar lunar ce. Manzo dai ya rasu a daidai ranar da aka haiheshi yana da shekaru 63 a duniya.

A daren wannan ranan Musulmi a fadin kasar Turkiyya n ayin addu’o’i , karatun Al-Qur’ani mai girma a gidajensu da kuma masallatai.
Continue reading...

ANYI KIRA GA AL'UMMAR MUSULMI DA SUYI KOYI DA HALAYEN MANZON ALLAH (SAW).

ANYI KIRA GA AL'UMMAR MUSULMI DA SUYI KOYI DA KYAWAWAN HALAYEN ANNABI MUHAMMAD (SAW).

Gwamnan Jihar Bauchi, Bala Mohammed, yayi kira ga Al'ummar Najeriya da su yi koyi da kyawawan halayen Manzon tsira Annabi Muhammad Sallallahu Alaihi Wasallam.

Gwamnan Bala, yayi wannan Kiran ne a lokacin da yake jawabin sa a ranar Asabar a wajen murnar zagayowar haihuwar Annabi Muhammad Sallalahu Alaihi Wasallam, Maulidi.

Ya bayyana cewar lizimtar kyawawan halayen Annabi ko Suffofin sa zasu iya kawo karshen wadan su matsalolin sa suka dabaibaye kasar nan.

Sanata Bala, ya kuma kira ga Al'umma suyi amfani da wannan lokacin mai Albarka na Maulidi don yin Addu'oi ga kasar mu Najeriya.

Allah Ya Saka Da Alkhairi, Allah Ya Ƙara Mana Soyayyan Manzon Allah (saw). Amiin

Continue reading...

Saturday, November 9, 2019

WANI SENATA YA BADA GUDUMMAWAR DIBINAI DA RUWA

MAULUDIN BANA: Sanatan Neja Ta Arewa Ya Bada Gudummawar Naira Dubu 400 Da Dabino Da Ruwan Gora Ga Mabiyar Darikar Tajjaniyya

Albarkacin ralin mauludin Annabin Rahama (S.A.W) da za'a gudanar a karamar hukumar Kontagora a gobe Lahadi, Maigirma Sanata Dakta Aliyu Sabi Abdullahi (Baraden Borgu) mai wakiltar Jihar Neja ta Arewa kuma mataimakin mai tsawatarwa na majalisar dattijai, yabada gudunmuwar Naira Dubu Dari Hudu (N400000) ga mabiya Darikatul Tijjaniyya na karamar hukumar Kontagora.

Sanatan ya mika wannan gudunmuwa ne ta hannun wakilin sa Alhaji Abubakar Dan Usman wanda shugaban Shababul Faila Malam Auwal Inuwa ya karba a madadin 'yan darikar.

Sannan ya sayi katan-katan na dabino da ruwan gora domin rabawa bayin Allah da suka halarci ralin.

Wannan dai ba shi ne karon farko da Sanatan ke bada irin wannan gudunmuwa ba domin duk shekara yana bada gudunmuwar sa domin gudanar da Mauludi. Hakazalika yana tallafawa sauran kungiyoyin addini a duk lokacin da wani hidimar addini ya tashi.

Sen.Barade Media Team.
09/11/2019.

Continue reading...

Friday, November 8, 2019

MAULUDIN ANNABI YAFI HUJJA

MAULUDIN ANNABI S.A.W YAFI QARFIN HUJJA.
.
Tare Da Umar Chobbe
.
PROFESSOR ibrahim maqari yana cewa:
.
Watarana an tambayi SHEIKH IBRAHIM INYASS menene hujjan yin MAULUD ?
.
Sai Shehu yace rashin Hujja Maulidi shine ya kawo hujjan mu na yin mauludin
.
Domin akwai Abunda yafi Qarfin hujja
Shehu yace baka ga duk Qur'ani, ba inda Allah yacema UWA ta so DAN ta ba?
.
Ai Allah bai cema UWA ta so DAN taba, saboda bata bukata sai ance mata ta so shi zata so shi. Domin Allah ya riga ya shuka son DAN acikin UWAN,
.
Amma shi DAN da a kasan zai iya Qin biyayya baka ga wuri daban daban Allah yake umartarsa da bin iyaye ba?
.
SHARHI:-
.
PROFESSOR IBRAHIM MAQARI yake cewa: Watarana an taba haduwa da wata mata aka nunamata wani malami "imamul Faharrazi" aka ce mata kinga malamin can zai iya baki Hujja dubu akan samuwan Allah
.
Sai matan tace "Allah sarki miskini!
.
Ai yana da shakka dubu ne a zuciyarshi shiyasa har zai iya samo hujja dubu in ba haka ba ya za'ayi mutum, in ba mahaukaci ba yadauko "touch light" da rana kuma yace wai yana neman Rana.
.
Duk girman hujja ai bata kai "touch light" rana tare da ubangiji ba, Allah da yakira kansa "Azzahiru" kuma yake bukatan wata hujja tazo ta bayyana dashi?
.
Ai Lamarin Akwai Abun dubawa.
.
Allah ya karawa malam lafiya da fahimta bijahi S.A.W. Amiin
Continue reading...

WANI SENATA YA BAWA MASU BIKIN MAULUDI GUDUMAWA

MAULUDIN BANA 1441:

Albarkacin ralin mauludin Annabin Rahama (S.A.W) da za'a gudanar a karamar hukumar Kontagora a jibi lahadi, Maigirma Sanata Dakta Aliyu Sabi Abdullahi (Baraden Borgu) yabada gudunmuwar Naira Dubu Dari Hudu (N400000) ga Ahlul Darikatul Tijjaniyya na karamar hukumar Kontagora.

Sanatan ya mika wannan gudunmuwa ne ta hannun wakilin sa Alhaji Abubakar Dan Usman wanda shugaban Shababul Faila Malam Auwal Inuwa ya karba a madadin 'yan darikar.

Wannan dai bashine karon farko da Sanatan ke bada irin wannan gudunmuwa ba domin duk shekara yana bada gudunmuwarsa domin gudanar da Mauludi, Hakazalika yana tallafawa sauran kungiyoyin addini a duk lokacin da wani hidimar addini ya tashi.

Allah Ya Saka Masa Da Alkhairi. Amiin
Continue reading...

SHIRYE SHIRYEN MAULUDI A JIHAR BAUCHI YA KAN KAMA

SHIRYEN SHIRYEN GUDANAR DA  MAULIDIN ANNABI (S.A.W) GWAMNAN JIHAR BAUCHI BALA MUHAMMAD YA WARE MILIYAN 100

Shirye-shiryen babban taro don tunawa da ranar haihuwar fiyayyen halitta Annabi Muhammadu (s.a.w) a jihar Bauchi

komitin da Maigirma Gwamnan jihar Bauchi sanata Bala Abdulkadir kauran Bauchi ya kafa na shirin fara rabon kyautan kayan masarufi ga Al'umman a jihar Bauchi.

Allah Ya Sa Ayi Taro Lafiya.  Amiin
Continue reading...